- Kada ku sanya ni cikin masu neman kujerar gwamna a 2023
- Babba dama ce gwamna Tambuwal ya bani
- Na mayar da hankalina ne kan aiki da aka sanya ni
Abdussamad Dasuki, kwamishnan kuɗi na jihar Sokoto yace baya daga cikin masu muradin tsayawa takarar gwamna a jihar a shekarar 2023.
Ya bayyana hakan ne ranar Litinin a yayin da yake bayani cikin wani shirin gidan rediyo kan nasarorin da gwamna Aminu Tambuwal ya samu wajen gudanar da gwamnatinsa.
Da yake amsa tambayar da aka yi mishi kan ko yana son fitowa takar gwamnan jihar Sokoto domin ya gaji me gidansa, sai Dasuki yace: “Bana cikin masu nema. Cire ni daga cikin masu neman kujerar gwamna a jihar a shekarar 2023.”
Karanta wannan: Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin masana’antar iskar gas a jihar Rivers

Dasuki yace ba ƙaramar dama bace muƙamin kwamishna da gwamna Tambuwal ya bashi domin sauyan fasalin tattalin arziƙin jihar gami da tabbatar cewa anyi aiki dashi yadda ya kamata don ya amfani ƴan jihar ta Sokoto.
Kwamishnan yace ya mayar da hankalin shi kacokan ne kan wannan aikin, saboda haka bazai karkatar da hankalin shi zuwa neman kujerar 2023 ba, kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Dasuki yayi kira ga duk masu ƙaunar jihar Sokoto dasu cigaba da mara ma gwamna Tambuwal baya kan ƙudurin da yake na ganin ya ɗora jihar kan turba me kyau don walwalar kowa da kowa.
Da yake magana kan nasarorin da Tambuwal yayi a cikin shekaru biyu da yayi akan mulki, kwamishinan yace Tambuwal ya ƙara ƙarfafa tattalin arziƙin jihar, ya kuma inganta tsarin biyan albashi, doɗe duk wasu ƴan matsaloli, sannan kuma ya sauya fasalin tattalin arziƙin jihar.
A wani labarin kuma, Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri yace salon sauya tsarin fasalin kasarnan da wasu ke hankoro na kan turba, don haka shi ma yana goyon baya ɗari bisa ɗari.
Har wa yau gwamna Fintiri ya ce muddin sauya fasalin kasar zai taimaka wajen gyaran targaden da kasar nan ke fama da shi, to babu shakka matakin aiwatar da hakan shine Alkhairi.
Da yake magana a yayin kaddamar da Asibitin kwararru mai daukan gadaje 220 dake birnin Asaba, Fintiri ya yaba da tsarin gudanar da mulkin gwamnan Jihar ta Delta Ifeanyi Okowa ta inda har yake kawo musu romon Dimokuraɗiyya.