- Tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya karyata rade-radin shirin sa na sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC
- Gwamnan G5 yace sauya sheka zuwa APC baya cikin ajandar taron da suka yi da Tinubu.
- Yace “mu ‘yan Najeriya ne kuma mun zo ne domin mu baiwa shugaban kasa goyon baya.
Tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa yana shirin sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC bayan ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Juma’a,Punch ta rawaito.
Wike, tare da Seyi Makinde da James Ibori sun gana tare da Tinubu domin ba shi goyon baya, kwanaki hudu bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Shiga Ganawa da Gwamnonin G5 a Fadar Gwamnati
Wike, jigo a jam’iyyar PDP, ya yi watsi da rade-radin cewa yana shirin komawa APC, ya kuma musanta cewa sauya sheka zuwa APC na cikin ajandar taron.
Da manema labarai suka tambaye shi ko sauya sheka zuwa APC na cikin ajandar taron da suka ya yi, Wike ya amsa da cewa: “A’a. Babu shiri. Babu wani abu makamancin haka.
“Mu ‘yan Najeriya ne kuma mun zo ne domin mu baiwa shugaban kasa goyon baya.
“Abin da ake bukata ke nan. Babu wani babban abu game da hakan.
A wani labarin kuma, Tallafi: Tinubu Ne Kadai Zai Iya Sanya Dokar Kayyade Farashin Man Fetur – Falana ga NNPCL
A wani labarin kuma,Lauyan dake kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya cewa Kamfanin NNPCL ba shi da hurumin tsayarwa ko daidaita farashin man fetur.
Falana ya cewa ikon kayyade farashin man fetur yana hannun shugaban kasa Bola Tinubu.
A ranar 31 ga watan Mayu, kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa ya daidaita farashin man fetur a kasuwannin sa.