Wani magidanci ɗan ƙasar Kenya mai suna James Jkorir ya koka kan yadda matar sa take hanawa suyi kwanciyar aure.
Magidancin ya bayyana cewa yayi nadamar auren matar sa saboda duk lokacin da ya nemi da suyi kwanciyar aure ta fake da cewa bata da lafiya. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Yadda wata mata ta rataye kanta tare da ɗanta
Magidancin ya nuna ɓacin ran sa ne dai a wani rubutu da yayi a wani dandali na mabiya addinin Kirista, a ranar Laraba 18 ga watan Janairun 2023.
A kalaman sa:
“Ya zanyi da matar da take ƙaryar bata da lafiya duk lokacin da na nemi muyi kwanciyar aure. Nayi nadamar kasancewa cikin wannan auren!!!”
Mutane da dama sun mayar da martani akan wannan maganar da magidancin yayi, inda da yawa daga ciki suka bashi shawarwari kan yadda zai shawo kan matsalar.
Ga kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
Israel Lawson ya rubuta:
“Ko dai baka san yadda ake yin aikin ba ko kuma kana ji mata ciwo ne. Ka zauna ka nutsu da kyau ka gano menene ba kayi daidai, sai ka zaunar da ita kayi mata alƙawarin cewa zaka gyara sannan kayi ƙoƙarin ganin ka gyaran.”
Grace Wambui Waturu ta rubuta:
“Wannan matsalar rashin tattaunawa ne. Ko da yaushe ina cewa bai kamata ma’aurata na ɓoye junan su wani abu ba.”
Yitzhak Babu ya rubuta:
“Matar ka ce. Kada kaji komai kayi mata magana kaji meyasa take yin hakan. Ka gaya mata yadda kake ji idan tayi hakan. Ta iya yiwuwa akwai yadda take son ayi aikin amma ba kayi daidai. A ɓangare ɗaya kuma ƙila tana samun abinda take so ne a wani wajen amma kada kayi saurin yanke hukunci ba tare da samun hujja ba.
Bayan Yayi Mata Fitsarin Kwance, Wata Budurwa Ta Ɗauki Wani Mummunan Mataki Akan Saurayinta
A wani labarin na daban kuma, wata budurwa tayi yunƙurin halaka saurayin ta bayan yayi fitsarin kwance a gadon da suke kwanciya.
Ana tuhumar wata budurwa a yankin East Baton Rouge, a birnin Louisiana, na ƙasar Amurka da laifin yunƙurin halaka saurayinta bayan ta caka masa wuƙa lokacin da yayi fitsari a kan gadon su.
Majiyar mu ta rahoto cewa jami’an ƴan sanda na East Baton Rouge, sun garzaya asibitin yankin bayan samun rahoton cewa an cakawa mutum wuƙa.