Ana tuhumar wata budurwa a yankin East Baton Rouge, a birnin Louisiana, na ƙasar Amurka da laifin yunƙurin halaka saurayinta bayan ta caka masa wuƙa lokacin da yayi fitsari a kan gadon su.
Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa jami’an ƴan sanda na East Baton Rouge, sun garzaya asibitin yankin bayan samun rahoton cewa an cakawa mutum wuƙa.
KU KARANTA KUMA: Wani magidanci ya siyar da gidan sa domin ginawa ɗiyarsa katafaren wajen wasa
Ana duba lafiyar matashin bisa raunin da ya samu a ɓangaren jikin sa na hagu da fashewar kunhu.
Matashin ya gayawa ƴan sanda cewa budurwar sa mai suna Briana Lacost, mai shekara 25, tayi matuƙar fusata bayan yayi fitsari a gadon su wanda suka kwashe shekara ɗaya da rabi suna kwana tare a kansa.
Rahoton ya kuma ƙara yin nuni da cewa Briana da saurayin nata sun fita shan barasa a dare ranar inda suka yi mankas.
Bayan yayi fitsari a kan gadon, matashin ya gayawa ƴan sanda cewa Lacost ta tayar da shi daga barci sannan ta fara dukan sa. Lokacin da yayi ƙoƙarin ƙwacewa daga hannunta sai ta bi shi ta caka masa wuƙa.
Jami’ai masu gudanar da bincike sun samu jin ta bakin Lacost, inda ta gaya musu cewa ita da saurayin nata suna shirye-shiryen rabuwa. Ta gaya musu cewa ta ji matuƙar haushi cewa saurayinta yayi fitsari akan gadon inda ta wullo daga kan gadon wansa hakan ya janyo ɓarkewar hatsaniya a tsakanin su.
Lacost ta kuma gaya musu cewa saurayin ta ya fara shaƙeta lokacin da suka faɗan, inta ta kare kanta ta hanyar caka masa wuƙa a ƙasan hannun sa na hagu. Tayi ƙoƙarin ta bashi magani amma daga baya sai ta kawo shi asibiti.
Ƴan sandan suna tuhumar Lacost da yunƙuran ɗaukan rai.
Wani Matashi Ya Nuna Sauyin Rayuwar Da Ya Samu Bayan Budurwarsa Ta Guje Shi
A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya nuna irin sauyin da ya samu bayan budurwarsa ta watsa masa toka a ido.
Wani matashi ya samu sauyi sosai bayan da budurwar sa ta gaya masa cewa bata son yanayin ƙirar jikin sa.
Matashin ya samu sauyi sosai a cikin wani bidiyo da aka sanya a manhajar TikTok wanda ya nuna yadda kamannin sa yake a baya da kuma yadda kamannin sa suke a yanzu.