- An sanya ran 22 ga Yuni a matsayin ranar sauraron ƙara
- Sunce matakin da gwamnati ta ɗauka tauye haƙƙine
- Wasu Ƴan Najeriya 420 sun mara ma matakin baya
Wata kotun al’umma dake ƙarƙashin ECOWAS ta tsayar da ranar 22 ga wannan wata na Yuni da muke ciki don sauraron ƙarar da SERAP da haɗin gwuiwar wasu ƴan Najeriya su 420 suka kai ka batun dakatar da Tuwita.
Daga cikin mutane 420 da suka shigar da wannan ƙara akwai Oby Ezekwesili, tsohuwar ministar ilmi kuma ɗaya daga cikin mutanen da suka assasa gangamin nan na #BringBackOurGirls tare da kuma fiyaccar ƴan gwagwarmayar nan Aisha Yesufu.
Alkaliyar da zata kula da wannan shari’ah wato Maimuna Lami Shiru ta bayyana ma lauyan masu ƙara Femi Falana SAN, cewa za’a saurari ƙarar ne tan hanyar amfani da fasahar sadarwa ta zamani.
Karanta wannan: Shugaban Jamus zai zamo shugaba na farko da zai ziyarci Sabuwar gwamnatin Isra’ila

SERAP da sauran masu shigar da ƙarar sunyi ƙorafin cewa matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na dakatar da Tuwita ya tauye haƙƙin dan Adam da kuma haƙƙin faɗar albarkacin baki da damar bayyana ra’ayi a shafukan zumunta da kowanne ɗan ƙasa yake dashi.
A ƙarar mai lamba ECW/CCJ/APP/23/21, an ɓuƙaci kotu ta dakar ta gwamnatin tarayya kan wannan ƙudira nata na hana tuwita a Najeriya tare da hana kowa da kowa kama daga kafafen watsa labarai zuwa gidajen talabishin yin amfani da kafar don isar da saƙonni, kamar yadda majiyar mu ta Tribune ta samu.
Masu karar sunce “muddun kotu bata yi ƙoƙarin dakatar da gwamnati ba cikin gaggawa, to lallai kafafen watsa labarai da gidajen talabishin da sauran makamantansu zasu fuskanci tsangwama matuƙa akan yin amfani da sahar.”
Sunce dakatar da tuwita dai anyi shi ne don kawai gwamnati ta samu damar toshe hanyoyin da ƴan Najeriya ke bi wajen binciko da fallasa bahallatsar da wasu jami’an gwamnatin ke aikatawa.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Jihar Kano za ta biya alawus din ma’aikatan jihar da suka mutu daga 2017 . Gwamnatin Jihar Kano ta ware sama da naira miliyan talatin a matsayin kudin alawus din ma’aikatan jihar 664 da suka mutu daga shekarar 2017 zuwa watan Fabrairun 2021.
Kwamishinan yada labaran Jihar Mallam Muhammad Garba shine ya tabbatar da hakan a tattaunawarsa da manema labarai a birnin Kano.
Ya ce gwamnatin ta yi la’akari da dokar ma’aikata ne da ta tanadi cewa tilas ne a biya iyalan ma’aikata da suka riga mu gidan gaskiya alawus din su don rage musu radadin rayuwa.
Kazalika a hannu guda kuma Kwamishinan ya ce Gwamnatin jihar ta ware kimanin sama da naira miliyan 20 wa tashar Radio Mallakar jihar wato Kano Radio Corporation don inganta yanayin aikinta.