Gwamnatin Jihar Kano ta ware sama da naira miliyan talatin a matsayin kudin alawus din ma’aikatan jihar 664 da suka mutu daga shekarar 2017 zuwa watan Fabrairun 2021.
Kwamishinan yada labaran Jihar Mallam Muhammad Garba shine ya tabbatar da hakan a tattaunawarsa da manema labarai a birnin Kano.
Ya ce gwamnatin ta yi la’akari da dokar ma’aikata ne da ta tanadi cewa tilas ne a biya iyalan ma’aikata da suka riga mu gidan gaskiya alawus din su don rage musu radadin rayuwa.
Kazalika a hannu guda kuma Kwamishinan ya ce Gwamnatin jihar ta ware kimanin sama da naira miliyan 20 wa tashar Radio Mallakar jihar wato Kano Radio Corporation don inganta yanayin aikinta.
Ya ce za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen samar da na’urar tsantsame ruwa, da na’urar dake samar da wuta da dai sauransu wanda hakan zai taimaka wajen inganta samar da na’urar dake aika labarai dake Jogana.
Ya ce lura da yadda na’urorin suka lalace ba tare da aiki ba, ya sa aka tsaida matsaya don alkinta su, la’akari da muhimmancinsu wajen aika sako wa al’ummar jihar.