Wani dan Najeriya ya yi kira ga cocinsa da su dawo masa da kudaden da suka nemi ya biya a matsayin na ginin gida a Aljanna, LIB ta ruwaito.
Kamar yadda ya bayyana a bidiyo tana shaidawa, tsawon shekaru fastonsu ja janyo masa ayar Bibul, Izifi na 6,
KU KARANTA: Wata coci ta buƙaci ‘yan jarida da su zama masu ƙwarewa da bin ƙa’idojin aiki
Matthew, aya ta 19 zuwa 21 inda aka bukaci ya saka hannun jari a cocin. Kamar yadda ayar ta nuna:
“Ku zuba tsadaddun abubuwa a duniya inda za su rube kuma su yi tsatsa, inda barayi zasu balle su sace.
“Amma ka yi wa kanka tanadi a lahira, inda babu abinda zai lalace ko ya yi tsatsa sannan barayi ba za su iya ballewa su sace ba.
“Domin lallai za ka adana tsadaddun abubuwan, kuma zuciyarka ma ta samu.”
Ya kara da cewa an yaudare shi da wadannan maganganun, hakan yasa ya dinga zuba kudadensa a coci.
Saidai a yanzu da yake mawuyacin yanayi kuma gwamnati ta kasa tabuka abubuwan arziki, sannan banki sun kasa samar da kudade, yana son fitar da kudaden da ya zuba a coci.
Ya ce akwai littafin da suke cikewa matsawar sun zuba kudi, kuma alamu na nuna makudan kudade ya kwashe shekaru yana zubawa.
Ya kara da cewa yana bukatar coci ta tattaro masa duk kudin da ya zuba, yanzu ya sauya ra’ayinsa na gina gida a Aljanna. Yana bukatar kudin don ya rayu a duniya.”
Yadda fasto ya umarci mambobin cocinsa su ci ciyawa matsawar suna son su shiga Aljanna
Yayin da fastoci suke ta sanya dokoki ga jama’a daban-daban kan hanyoyin shiga Aljanna da kuma hanyoyin da zasu kauce wa wuta, wani fasto ya ba da nashi, DJ Biomo Promotions ta ruwaito.
A cewarsa ya kamata su ci ciyawa tamkar shanu matsawar suna don su shiga Aljanna. Kuma ba su isa su kauce wa dokar Ubangiji ba.
Ya bayyana cewa ya yi magana da Ubangiji inda ya ce duk wanda bai yarda da maganarsa ba mai zunubi ne.
Don haka ya bukaci matsawar suna son su shiga Aljanna, sai sun cinye ciyayi tamkar dabbobi. An samu bayani a kan cewa faston dan kasar Afirka ta kudu ne.