Yayin da fastoci suke ta sanya dokoki ga jama’a daban-daban kan hanyoyin shiga Aljanna da kuma hanyoyin da zasu kauce wa wuta, wani fasto ya ba da nashi, DJ Biomo Promotions ta ruwaito.
A cewarsa ya kamata su ci ciyawa tamkar shanu matsawar suna don su shiga Aljanna. Kuma ba su isa su kauce wa dokar Ubangiji ba.
KU KARANTA: A matsayina na fasto ina da damar ɗirkawa duk macen da naga dama ciki
Ya bayyana cewa ya yi magana da Ubangiji inda ya ce duk wanda bai yarda da maganarsa ba mai zunubi ne.
Don haka ya bukaci matsawar suna son su shiga Aljanna, sai sun cinye ciyayi tamkar dabbobi. An samu bayani a kan cewa faston dan kasar Afirka ta kudu ne.
Daya daga cikin mambobin cocin, Gilbert ya bayyana cewa:
“Sai da muka ci ciyawa kamar shanu saboda haka faston mu yace. Ba za mu iya kyauce wa fadin Ubangijinmu ba.
“Yana magana da Ubangiji kuma masu zunubi ne kadai ba za su fahimci abubuwan addini ba su yi tunanin ba daidai bane.”
FBI, Da ‘Yan Sanda Na Farautar Wadanda Suka Yi Ajalin Matar Faston Najeriya
Hukumar Bincike ta Tarayya da ‘Yan sandan New Jersey sun fara wani aiki na hadin gwiwa domin bankado sirrin da ke tattare da mutuwar wata ‘yar majalisar Republican, Eunice Dwumfour.
Jaridar New York Post ta ruwaito cewa an harbe Dwumfour har lahira a gaban gidanta da ke New Jersey, a Amurka, a ranar Larabar 1 ga watan Fabrairun 2023.
Dwumfour, mai shekaru 30, an bayar da rahoton cewa wani maharin da har yanzu ba a san ko wanene ba an buge ta a lokacin da take tuka mota a gidanta.