Wani ma’aikacin gidan ruwa Mai kimanin shekaru 37 a daren laraba ya ƙone wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa yayin da motarsu ta kama da wuta.
Marigayin mai suna Emmanuel ma’aikacine a gidan ruwan Softfort Table Water Wanda yake a layin Obanisuwa Egbejila akan titin Airport dake ilorin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hadaddiyar Daular Larabawa Da Najeriya Sun Tattauna Kan Fadada Hadin Gwiwa Tsakanin Tattalin Arzikin Kasashen Biyu
Majiyar Jakadiya, ta bayyana cewa, Yana kan hanyarsa ta koma wa daga gidan Mai zuwa kamfanin, inda motar sa Mai Lamba LSR966GD ta kama da wuta.
Shugaban mamacin Mai suna Mr Surajudeen, ya bayyana cewa lamarin ya faru da misalin Karfe 9:00 na dare, dai-dai lokacin da wasu jarakuna guda 3 mai nauyin kilomita 30 na Fetur, a cikin motar, wanda sun fashe ne, saboda ƙarancin iska.
Da yake tabbatar da lamarin a daren ranar Alhamis, Shugaban hukumar Kashe gobara na Jahar kwara, Hassan Adekunle ya bayyana cewa lokacin da lamarin ya faru duka kofofin motar sun rufe.
Sai daga baya jami’anmu sun gano gawar a cikin motar, bayan sunje wurin da lamarin ya faru.
A cewar Daraktan hukumar Kashe gobara, Prince Falade Olumuyiwa , ya jajantawa Iyalan mamacin yayin da yayi Kira ga sauran Al’umma dasu ɗauki matakan kariya da mahimmanci.