An ba wa BBC damar ci gaba da gudanar da ayyukanta a Burundi shekaru uku bayan da aka dakatar da ita daga kasar.
Hukumar kula da harkokin yada labarai ta kasar Burundi gami da Majalisar Sadarwa ta kasar (CNC) – suka bayyana hakan bayan wani taro a ranar Laraba a birnin kasuwanci na Bujumbura.
An dakatarwa da BBC lasisin ta ne a ranar 29 ga Maris din shekarar 2019 – kuma babu wani dan jarida da aka yarda ya yi aiki ko aika bayanai ga kafar yada labaran.
Hakan ya biyo bayan rahotannin da BBC ta yi, Wanda Mahukunta a kasar ke ganin cewa ta lalata sunan gwamnatin marigayi shugaba Pierre Nkunrunziza – musamman wani bincike da aka yi kan wasu wuraren azabtarwa na sirri da aka yi amfani da shi wajen dakile ‘yan adawa, wanda gamnatin kasar ta yi watsi da shi a matsayin “labaran karya”.
A lokacin haramcin Burundi na da masu kallo da sauraren BBC akalla miliyan 1.3 a kasar.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun yi Allah-wadai da matakin, yayin da kungiyar Amnesty International ta ce ta kafa wani Kwamiti da zaiyi bincike kan “kokarin da mahukuntan Burundi ke yi na rufe kafafen yada labarai”.
Shugabar CNC, Vestine Nahimana, ta shaidawa manema labarai cewa majalisar ta dauki matakin barin gidan rediyon BBC ya fara aiki nan take bayan wata bukata daga gidan rediyon.
Ta bayyana cewa shugaba Évariste Ndayishimiye ne ya fara sassauta takunkumin da aka sanyawa kafafen yada labarai.
Shugaban na yanzu, wanda shi ne zababben magajin Mista Nkunrunziza, ya hau karagar mulki bayan ya lashe zabe a shekarar 2020 – ‘yan watanni kafin lokacin da aka yi zato yayin da Mista Nkunrunziza ya mutu a kan karagar mulki.