Mutane 18 ne suka mutu sannan wasu akalla 15 suka jikkata a wani hari da wasu mutane dauke da makamai suka kai a Fentalle, wani yanki na dake Gundumar Oromia na kasar Habasha.
Wadanda suka mutun sun hada da jami’an ‘yan sandan tarayyar kasar uku da wasu ‘yan bindigar da ke dawowa daga wani samame kamar yadda wani shugaban yankin Ababu Wako ya bayyana.
Har yanzu dai ba a bayyana dalilin da ya haddasa harin ba, kuma a halin yanzu ana gudanar da bincike.
Hukumomin yankin na zargin wasu mutane dauke da makamai daga yankin da ke makwabtaka da su ne suka haddasa lamarin.
An dade ana taf ka takaddama kan iyakokin yanki a kasar ta Habasha.
A wani labari Kuma na daban.
Kaduna: El-Rufai ya gargadi al’umma game da kare Yan bindiga bayan sun kai hari
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya gargadi al’umma da su guji baiwa wadanda ake zargi da aikata muggan laifuka kariya a tsakanin su yayin da gwamnati ke kokarin magance matsalar rashin tsaro a fadin jihar.
El-Rufai ya yi wannan gargadin ne a ranar Larabar, a lokacin da ya ziyarci Sarkin Kagoro, Mista Ufuwai Bonet, a fadarsa da ke karamar hukumar Kaura, domin jajantami shi kan harin da aka kai a yankin kwana-kwanan nan.
Hakan na zuwa ne kasa da ‘yan kwanaki bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wani jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta Abuja zuwa Kaduna.
“Abun takaici ne kannyadda al’ummomi ke kare masu aikata laifuka da ke zaune a cikinsu. Akwai masu laifi a kowace kabila da kowane addini.
“Idan muna son kawo karshen irin wannan matsalar (rashin tsaro), dole ne mu kasance a shirye mu rabu da wadanda muke zargi da aikata laifuka ko da ‘ya’yanmu maza ne mata,” inji gwamnan.
A cewarsa, zaman lafiya za a samu ne kawai idan al’ummomi suka mutunta hukumomin da aka kafa tare da kai rahoton wadanda ake zargi ga hukumomin tsaro.
“Wannan ita ce hanya daya tilo da za mu iya rayuwa cikin kwanciyar hankali,” in ji shi.
El-Rufai ya bukaci sarakunan gargajiya da su kara kaimi wajen sauke nauyin da ke kansu na samar da shugabanci.
“Idan har hukumomin gargajiya da sauran jami’ai ba za su iya samar da shugabanci ba, to za mu iya murkushe su mu mika ragamar shugabancin ga matasa idan har hakan ne zai kawo zaman lafiya.
“Ina so in yi kira gare da ku da ku tashi tsaye wajen ganin kun gudanar da ayyukan ku na jagoranci kamar yadda ya dace, kuma kun sanar da mu wadanda ke da hannu wajen aikata laifuka domin mu magance su,” in ji shi.