Bayan shekaru 5, Ƴan Sandan Imo sun kama Bokan daya kashe Sufeton Rundunar
Rundunar Ƴan Sandan Jahar Imo a ranar Alhamis yace ta kama Boka da yaran sa, da ake zargin sun kashe wata Sufeto na Ƴan Sanda Felicia Nwagbara.
Wannann na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Micheal Abattam ya Fitar a Owerri, Babban Birnin Jahar, yana mai cewa Rundunar ta nemi Ƴar Sandan ta rasa a Shekarar 2017.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ana Fargaban Wani Manjo Ya Harbe Kansa A Jihar Kaduna
Abattam yace an kama su ne a Agwa Ƙaramar Hukumar Oguta ta Jahar, wanda sashen Kwararru ta Rundunar.
Yace baya ga Kisan Jami’ar, sun kasance suna haɗa kai da ƴan ta’adda da masu garkuwa da mutane, da suke kai hari a Jahar.
Abattam ya sanar da sunayen wanda ake zargi da suka haɗa da Casmire Mgbugha mai shekaru 53, da Hycent Chimezie mai shekaru 39, da Hycent mai shekaru 28, da Hycent Ifesinachi mai shekaru 26, da Hycent Chimobi mai shekaru 23, da kuma Chukwuemeka Wisdom Mai shekaru 22 da kuma Nnadike Clifford mai shekaru 72.
Comments 1