Wani matashi ɗan Najeriya ya ba wata mata mamaki ta hanyar bata kyautar naira dubu ɗari (N100k) a matsayin kuɗin diyyar satar alawar da yayi mata shekaru da dama da suka wuce.
Matashin mai suna Theo Ayomoh, ya ziyarci shagon ta sannan ya siya biskit. Daga nan sai ya gabatar da kan sa a matsayin yaron da ta kama yana mara satar alewa lokacin yana ɗan shekara takwas a duniya, jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA: Hukumar Alhazai ta aike da wani muhimmin gargaɗi ga maniyyatan bana
Ya gaya mata cewa wannan ba shi bane karon farko da yayi mata sata kawai dai ta samu sa’ar kama shi ne a lokacin.
Theo ya yabawa matar da tayi masa nasiha a lokacin maimakon kai ƙarar sa a wajen iyayen sa. Daga nan sai ya ɗuka ƙasa kan guiwoyin sa ya gode mata.
Hakan ya zo ne bayan ya ba matar kyautar N100k domin gode mata. Matar ta kaɗu matuƙa sannan tayi ta ƙwarara masa addu’o’i.
Ku kalli bidiyon a nan
Bidiyon ya sosa zukatan mutane sosai a soshiyal midiya.
Ga kaɗan daga cikin abinda mutane suke cewa dangane da bidiyon waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
@monicaihezuoh ta rubuta:
“Rayuwar yarinta, muna yiwa iyayen mu sata, na rasa gane meyasa muke yin hakan.”
@Faith Macauley ta rubuta:
“Ka birge ni, Allah zai albarkace ka dan Allah ina son mu ƙulla ƙawance.”
@Dondaddy007 ya rubuta:
“Ɗan’uwana Allah zai albarkace ka saboda hakan da kayi. Kana da zuciya mai kyau.”
@Hyajide ya rubuta:
“Ka sanya na ji ƙwalla, Allah yayi maka albarka sannan muna godiya Mama.”
Wata Matar Aure Ta Koka Bayan Mijinta Ya Lallaba Yayi Mata Kishiya a Boye
A wani labarin na daban kuma, wata mata ta koka bayan mijinta yabi ta bayan fage yayi mata kishiya.
Wata mata ƴar Najeriya mazauniyar ƙasar Amurka ta koka a soshiyal midiya kan mijinta wanda suka kwashe shekara 12 tare a aure wata mata daban ba tare da sanin ta ba.
Matar mai suna Oyindamola wacce ta haifi ƴaƴa uku tare da mijin nata, ta bayyana a shafin ta na Instagram yadda mijinta da tayi tunanin suna cikin farin ciki ya auri wata daban a Najeriya ba tare da sanin ta ba.