Wata mata ƴar Najeriya mazauniyar ƙasar Amurka ta koka a soshiyal midiya kan mijinta wanda suka kwashe shekara 12 tare a aure wata mata daban ba tare da sanin ta ba.
Matar mai suna Oyindamola wacce ta haifi ƴaƴa uku tare da mijin nata, ta bayyana a shafin ta na Instagram yadda mijinta da tayi tunanin suna cikin farin ciki ya auri wata daban a Najeriya ba tare da sanin ta ba. Shafin Yabaleftonline ya rahoto
KU KARANTA KUMA: Daga zuwa wajen bauta, fasto yayi awon gaba da wayoyin masu ibadah
Oyin ta bayyana cewa ta fara shan jinin jikinta ne lokacin da taga wani baƙon sako a wayar mijinta lokacin suna yawon shaƙatawa a Dubai cikin watan Afrilun 2022.
“Duk lokacin da na ga hotunan ta, ina jin baƙin ciki.” A cewar saƙon
Ta bayyana cewa ta yiwa mijinta magana akan saƙon amma sai ya basar kawai yace wata mata ce kawai take son takurawa rayuwar sa.
Sai dai, bayan sun koma ƙasar Amurka tare da mijinta, sai ta duba wayar sa inda ta gano wata baƙuwar lamba wacce ta ke yawan kiran sa.
Tace ta kira lambar amma sai matar ta musanta cewa akwai wata alaƙa tsakanin ta da mijinta.
Abinda bata sani ba shine matar mai suna, Bunmi Adedapo, ta aure mata miji tun shekarar 2021.
Bayan ta ƙara bincike sai ta gano cewa mijinta da ya gaya mata cewa yaje Najeriya ne domin gudanar da wani aiki, ashe ya sulale ne yaje wajen sabuwar matar sa.
Tabdijam: Yadda Uba Ya Gwada Diyarsa Domin Gano Ko Tana Sana’ar Gidan Magajiya a Makaranta
A wani labarin na daban kuma, wani uba ya yiwa ɗiyar sa wani gwaji domin gano ko tana sana’ar karuwanci a makaranta.
Wani magidanci ɗan Najeriya ya gwangwaje ɗiyar sa da kyautar maƙudan kuɗaɗe bayan yayi mata gwajin kwantawa da wani saboda N300k.
Da yake magana da Shuga Plum, wani mai ɗaukar bidiyo, mutumin yace yana ganin maza ke ɗaukar ƴanmata sannan yana son ya san halayyar ɗiyar sa a makaranta.