By Abbas Yakubu Yaura
Hukumomin ‘yan sandan jihar Bayelsa sun tabbatar da kama wani matashi dan shekara 35 mai suna Kelvin Ekuere dake unguwar Koluama a karamar hukumar Ijaw ta kudancin jihar Bayelsa tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da kama shi, ya ce an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin a lokacin da ake masa tambayoyi, ya yi ikirarin yana aiki da wani Tibiebi Woinemi Amadein, wanda kani ne kuma babban jami’in tsaro na Sanata mai wakiltar Bayelsa ta tsakiya a jihar, Sanata Cleopas Moses da kuma mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP a jihar.
An kuma tattaro cewa ana kuma binciken wanda ake zargin bisa zarginsa da hannu a yunkurin sace wani Cif Patrick Ekubo da bai yi nasara ba a unguwar Akenfa 3 dake unguwar Yenagoa, babban birnin jihar.
Kazalika jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa duk da jerin gayyata da ‘yan sanda suka yi masa, mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP ya kasa amsa gayyatar ko bada wani rubutaccen bayani kan rashin zuwansa.
Comments 1