Bayern Munich na bukatar cin wasa biyu nan gaba daga hudun da suka rage a ba ta kofin Bundesliga na takwas a jere bayan da ta doke Bayer Leverkusen ranar Asabar kamar yadda Bbc suka labarto.
Bayern ta ziyarci Leverkusen ne a wasan mako na 30 a gasar Bundesliga, karawa ta hudu tun lokacin da aka ci gaba da gasar, bayan da cutar korona ta dakatar da wasanni a watan Maris.
Kungiyar da Hans Flick ke jan ragama ta yi rashin nasara a wasa daya tal daga 21 a baya a dukkan fafatawa a bana, Leverkusen ce ta fara cin kwallo daga baya ta farke ta kara uku.