Kakakin majalisar jihar Legas, Mudashiru Obasa, a jiya ya bayyana gaban kwamitin binciken majalisar bisa zarginsa da rashawa da wata kafar watsa labaran sakar sama ta yi.
Kakakin ya shaidawa kwamitin binciken cewa zarginsa da rashawa karya ne, kuma aiki ne na makiya.
Ya bayyana gaban kwamitin ne da Victor Akande mai wakiltar Ojo I ke yiwa jagoranci.
Wata kafar watsa labarai ta sakar sama ta bankado yadda Kakakin majalisar ke amfani da lambar asusu 64 a bankuna daban-daban wanda duk suke da alaka da lambar sirri ta bankinsa wato BVN.
Kafar watsa labaran ta ce asusun bankin na da sunannaki daban-daban wanda ake amfani da su wajen sace kudaden al’umma.
Kakakin majalisar ya ce batun siyan motoci da aka yi ga ‘yan majalisar wanda ya jagoranta, an yi shi ne bisa ka’ida a karkashin shirin FMU kuma sai da majalisar jihar ta amince.
Kuma batun cewa an kashe naira miliyan 258 wajen buga katin gayyata na kaddamar da majalisar ta 9, sam ba gaskiya bane.
Har wala yau kwamitin ya gayyato wadansu jami’an Bankin Zenith domin gabatar da bayani. Inda suka tabbatar da cewa Obasa asusun banki shida kawai yake da shi da bankin. Kuma ba zai yiwu mutum guda ya yi amfani da sunannaki daban-daban ba da lambar sirri ta banki wato BVN da yaba.