
Bazamu sanya hannu ba a bashin da bai da anfami, Ahmad Lawan
Shugaban Yan Majalisun Najeriya yace zasu sanya hannu ne akan bashin da sukan dalilin ciwo bashin da Kuma aikin da za’ai dasu.
Ahmad Lawan ya bayyana hakane Jim kadan bayan sun tattauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan abubuwa masu amfani ga Najeriya.
KARANTA:- Bada jimawa ba zamu kawo karshen ta’adancin a Najeriya
Yace Yan Majalisun zasuyi duba dakyau kamin su amince da bashin da duk wani yake bukatar karbowa.
Yace duk lokacin da aka kawo bukatar hakan zaai dogon bincike sannan zasu cigaba da bin diddigin aikin da za’ai dasu.
Yace kasar Najeriya ba kasa bace wadda take wadatatta duba da yadda muke rayuwa da kuma duba da abubuwan dake aukuwa a kasar yanayin harajin kasar yayi kadan don haka dole ne mu duba wajan yin ayyuka masu muhimmanci.