• Hadarin jirgin sama ya kashe mutun 10 a Kenya. inda mutun 13 suka sami mummunan rauni.
• Ma hukunta kasar sun tabbatar da afkuwar lamarin.
• Ankai wadan da sukaji rauni asibitin sojin kasar domin duba lafiyar su, inda tawagar binciken kasar ta Isa inda lamarin ya afku.
A kalla sojin kasar Kenya 10 ne su ka mutu a jiya Alhamis, sanadiyar hadarin da wani jirgin sama, lokacin da ya ke kokarin sauka a Nairobi baban birnin kasar, kamar yadda rundunar sojin da kafafen yada labaran kasar su ka bayyana.
Jirgin saman sojin kasar na Kenya kirar Mi 171 E, ya fadi ne da misalin karfe 9 na safe a Kajiado, kamar yadda sanarwar da rundunar ta fitar, Ina ta ce, mutun goma sun mutu, 13 Kuma sun sami mummunan rauni.
KARANTA WANNAN LABARIN: Haryanzu a ya yi na a masana’antar Kannywood
Inda sanarwar ta kara da cewa, wadan da suka sami raunukan an kai su asibitin sojin kasar dake Nairobi, domin duba lafiyar su .
Kuma tuni tawagar binciken kan hadarin jirgin sama na kasar, suka isa inda lamarin ya afku.
Kazalika mahukunta kasar sun ce, sojin dake cikin jirgin, na kan wani atisayi ne.
Comments 1