- Bazan ƙara zuwa wajan Buhari ba, inji Wike
- Gwamnan jihar Rivers ba zai sake kaiwa Buhari ziyara ba.
- Wike ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yana mayar da martani kan maganar Buhari da yayi yake cewa “wasu gwamnoni suna yawan zuwa Villa don samun mafita ga tsaron jahar su.
Mai magana da yawun Wike, Kelvin Ebiri a kafan sada zumunta yace ” ai da Buhari ya bayyana sunan gwamnonin da suke zuwa wajansa.
KARANTA:- sun datse kan mai Gadi lokacin da zasu shiga Gidan wani Ɗanmajilisa
Ya kara da cewa Shugaban Buhari da ya daina ɗorawa gwamnoni aikin da ba nasu ba.
Ya sake cewa “Shugaba Buhari shine Jagoran Jami’an tsaron ƙasa don haka bazai yiwu da ya dunga ɗorawa gwamnoni nauyi tsaron jihar su.
Gwamna Wike ya ƙara da cewa ” Buhari ya gayawa ƴan ƙasa ya gaza kan matsalar tsaron ƙasar da ya daina ɗorawa gwamnoni.”
Ya cigaba da cewa “Buhari kaine Jagoran jami’an tsaron na ƙasa kai ka zabi shugaban sojojin sama, ka zabi shugaban sojojin Ruwa, ka zabi shugaban sojojin ƙasa, ka zabi shugaban ƴan sanda da sauran duk wani nau’i masu bada tsaro. Mu suwa muka zaɓa, kuma yaya waɗanda Shugaba ƙasa ya zaɓa su zama ƙarƙashi na.
A cewarsa bawai an zaɓe ka bane ka dunga ciwo ma ƙasar najeriya bashi da kula da harkokin tsaro. Waya amince da hakan gwamnoni ko kai? Bawai dan matsalar tsaro yayi ƙamari kace kai alhakin gwamnoni ne.
Wike ya ƙara da cewar jam’iyyar APC bazata iya cikawa ƴan najeriya alkawarin da ta ɗauka ba.
Yace Nagode ma Allah da yasa bana daga cikin gwamnoni da suke kai koke su gareshi. Yace Ni a matsayi na na gwamnan jihar Rivers bazan taba yin hakan ba