Mai horas da ‘yan wasan Real Madrid Zinedine Zidane ya bayyana Karim Benzema a matsayin dan wasan da ya ke wani matsayi na daban a harkar tamaula.
Benzema ya ci kwallo daya ya kuma taimaka aka saka biyu a raga a wasan da Madrid suka lallasa Eibar 3-1 a ranar Lahadi a gasar La Ligar kasar Sipaniya.
Wannan ne karo na 30 da Benzema ya ke taimakawa a ci kwallo bayan ya ci a cikin wasan La Liga. Cristiano Ronaldo ne kawai ya dara shi, da gudummawa har sau 44, fiye da kowane dan wasan Real Madrid a karni na 21.