Yayin da ake dakon rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban Amurka a ranar Laraba, tawagar zaɓaɓɓen shugaban ta bayyana jerin dokokin da Trump ya sanya da yake shirin sokewa a ranar da aka rantsar da shi.
Shugaban ma’aikata na Mista Biden Ron Klain ya ce da zarar an rantsar da Biden, zai mayar da Amurka cikin yarjejeniyar sauyin yanayi, sannan ya soke haramcin shiga kasar daga wasu kasashen musulmai da shugaba Trump ya sanya.
Yanzu haka dai yawan dakarun da aka jibge a birnin Washington domin tabbatar da an yi bikin rantsuwar lafiya ya ninninka yawan dakarun kasar a kasashen Afghanistan da Iraqi.
Dukkanin jihohin Amurka 50 da Gundumar Columbia na cikin shirin ko ta kwana saboda yiwuwar samun zanga-zanga a karshen makon nan, gabanin bikin rantsar da sabon shugaban kasar Joe Biden a ranar Laraba.
Ana aikewa da dakarun Tsaro na kasa daga ko’ina cikin kasar zuwa Washington DC, domin dakile barazanar maimaita mummunar tarzomar da ta faru a ranar 6 ga Janairu.
Hukumar tsaro ta FBI ta yi gargadin cewa magoya bayan shugaba Trump na shirin yin zanga-zanga dauke da makamai a dukkan jihohin kasar.
An kafa shingayen binciken ababen hawa kan titunan babban birnin kasar cikin tsauraran matakan tsaro.
A ranar Asabar ne yan sanda suka tabbatar da kama wani mutumi dan jihar Virginia da bindigogi da harsasai 509 da kuma lasisin shiga taron rantsuwar na bodi.
Wadanne matakai jihohi ke ɗauka?
Jihohi a duk fadin kasar na daukar matakan kariya, kama daga kan hana zuwa Washington da kuma kin bayar da iznin gudanar da taro.
Gwamnonin Maryland, da New Mexico da Utah duk sun ayyana dokar ta-baci gabanin yiwuwar samun zanga-zangar.
Jihohin California, da Pennsylvania, da Michigan, da Virginia, da Washington da Wisconsin na daga cikin jihohin da aka baza jami’an tsaro na tarayya a ko ina.
A cewar darakta a Ma’aikatar Tsaron Jama’a ta Texas, bayanan sirri sun nuna cewa “masu tsattsauran ra’ayi” na iya kutsawa cikin zanga-zangar da aka shirya don “aikata muggan laifuka”.
Gwamnan Virginia Ralph Northam ya fada wa taron manema labarai a ranar Alhamis cewa: “Idan kuna shirin zuwa nan ko zuwa Washington da mummunar niyya to ya kamata ku sauya tunani, don ba a maraba da ku a nan, kuma ba za a yi maraba da ku ba a babban birnin kasarmu ba, idan kunne ya ji, gangar jiki ta tsira”
Daya daga cikin jihohin da aka fi tunanin samun rikici a cikinsu ita ce jihar Michigan, wadda tuni ta kafa shinge mai kafa shida a kusa da fadar gwamnatin jihar da ke Lansing.
-Rahoton BBC Hausa