Wata mata ƴar Najeriya wacce ta samu mijin aure a tana da shekara 68 a duniya, ta sanya mutane yin maganganu daban-daban a yanar gizo.
A cikin bidiyon, an nuna matar tana cikin farin ciki yayin da shirya tsaf cikin shiga irin ta amarya. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Tinubu da Mai Dakinsa Sun Diro Najeriya Daga Ƙasar Turai
An nuna abubuwa sosai a cikin ɗan gajeran bidiyon wanda ya nuna lokacin da ta ke yin ƙwalliya da lokacin da ta ke tiƙe da jan fure yayin da ta ke ɗaukar hoto.
Ƙayatacciyar kwalliya da aka yi mata ta sanya fuskarta ta ƙara bayyana kyawun ta, inda ta tsaya a gaban kyamara aka yi ta gwangwaje ta da hotuna domin nuna cewa ta samu rabin ran ta.
Mutane da dama sun nuna kaɗuwar su kan yadda aka yi ta samu miji da waɗannan shekarun na ta.
Bidiyon ya yaɗu sosai inda mutane da dama suka riƙa yin sharhi a kan sa.
Yadda Wani Dalibi Ya Dinga Tikar Rawa A Cikin Aji Ana Tsaka Da Koyar dasu, Bidiyon Ya Girgiza Internet
A wani labarin na daban kuma, wani bidiyon wani dalibi yana tiƙar rawa a gaban malamar sa a cikin aji ya ɗauki hankula sosai.
Wani bidiyo mai tsawon daƙiƙa 20 da aka saka akan shafin TikTok ya nuna yadda wani ɗalibi ke tikar rawa a cikin aji yayin lokutan makaranta.
Abin da ya sa bidiyon ya fara yaduwa shi ne, wata malama tana cikin ajin tana rubutu akan allo yayin da dalibin ke tikar rawa.