A wani lokaci can baya, wani ɗan Najeriya ya siya fili mai girma eka 10 sannan ya bayar da jinginar ta ga wasu manoma.
Dalilin sa na yin hakan shine yana da sauran abubuwan da ya ke yi kuma bai shirya ya fara aiki a cikin gonar ba. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Tinubu da Mai Dakinsa Sun Diro Najeriya Daga Ƙasar Turai
Sai dai, lokacin da ya tashi buƙatar gonar sa, sai ya dawo ya tarar da wani jan aiki a gaban sa, inda manoman suka bijire suka tafi wajen boka.
Dukkanin manoman sun haɗa kai sun yi amfani da asiri domin tabbatar da cewa bai amshi gonar daga hannun su ba.
Etubo Lion shine ya bayyana labarin a Twitter inda ya ke cewa:
“Yanzu wani ya gayamin labarin yadda ya siya fili mai girman eka 10 a Najeriya sannan ya bayar da shi ga manoma tunda baya da shirin amfani da filin a lokacin. Daga nan sai manoman suka fara amfani da asiri saboda ba su san tashi daga filin na sa lokacin da ya ke son ya fara aikin sa a filin.”
“Idan da kun ga irin abinda suka sanya idanun sa na gani filin na sa ehn? Ina ta cewa “omoooo”. Ina labarin irin matsalar fili amma omooooooooo. Tab ɗi Omooooooooooo.”
Bidiyon Matar Da Ta Yi Auren Farko Tana Da Shekara 68 a Duniya Ya Bar Mutane Baki Bude
A wani labarin na daban kuma, wata mata ta samu mijin aure tana da shekara 68 a duniya, bidiyon ta ya ba mutane mamaki sosai.
Wata mata ƴar Najeriya wacce ta samu mijin aure a tana da shekara 68 a duniya, ta sanya mutane yin maganganu daban-daban a yanar gizo.
A cikin bidiyon, an nuna matar tana cikin farin ciki yayin da shirya tsaf cikin shiga irin ta amarya.
Comments 1