Wata budurwa ƴar Najeriya ta ɗauki hankulan mutane da dama bayan ta nuna kayayyakin da mijin da zata aure ya kawo a matsayin kayan sadaki.
Budurwar ƴar Najeriya ta bayyana irin sha tara ta arziƙi da wanda zata aura ɗin ya kawo domin biya a matsayin kuɗin sadaki. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KARANTA KUMA: Ɗan Najeriya yayi wuff da kyakkyawar baturiya, har ta kai shi ganin iyaye
A cikin bidiyon wanda wani mai amfani da @amyspecialabacha2 ya sanya a manhajar TikTok, an nuna budurwar cikin ƙasaita ta ɗauki hoto a cikin tulin kayan sannan ta yabawa mijin da zata aura kan yadda ya zo cikin shiri domin biyan kuɗin auren ta.
Budurwar ta bayyana masoyin nata a matsayin jajirtaccen namiji sannan ta taya kan ta murna saboda ta kusa shigewa daga ciki.
Daga cikin abubuwan da ta nuna, akwai tuƙeƙen rago, buhun shinkafa, kayan sha, kayan kwalliya, akwatuna, kayan masarufi da dai sauran tulin kaya.
Ku Kalli bidiyon a nan
Bidiyon ya ɗaukin hankulan mutane sosai inda suka taya budurwar murnar kawo kuɗin aurenta da akayi babu ɗan gwashe.
Ga kaɗan daga ciki:
user5127659132436 ya rubuta:
“Ina matuƙar taya ki murna yar’uwa.”
LOVETH OMOKARO ta rubuta:
“Na wa ooo.”
Becca ta rubuta:
“Na taya ki murna sosai.”
Budurwa Ƴar Afrika Tayi Wuff Da Wani Bature, Ya Biyota Har Zuwa Ƙauyensu
A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ƴar Afrika tayi wuff da wani bature, har ya baro ƙasar su ya biyota zuwa ƙauyen su.
Wata budurwa tayi wuff da wani bature wanda har ya baro inda yake rayuwa ya zo garin su.
Bidiyon wanda aka sanya a TikTok ya nuna yadda baturen ya baro ƙasar su domin haɗuwa da ƴan’uwan masoyiyar sa.
Wani mai amfani da Cafe Au Lait shine ya sanya bidiyon, inda baturen yake cewa yana jindaɗi da kuma tsoron yadda zata kaya