Wata mata ta shiga cikin tashin hankali bayan da motarta, da rahotanni suka bayyana cewa ta siya akan Naira Miliyan Tara (N9m), ta kama da wuta, ta kone kurmus.
Rahotanni sun bayyana cewa matar ba ta jima da siyan motar ba, kirar Mercedes Benz, amma haka nan tana ji tana gani wuta ta kona motar kurmus.
A cikin wani bidiyo da ya ke ta yawo a kafofin sada zumunta na zamani, an ga wata mata tana nuna farin cikinta bayan da ta biya miliyoyin kudi ta sayawa kanta sabuwar motar.
Sai dai bayan watsa hotunan motar a shafukanta na sada zumunta, motar ta kama da wuta a wannan ranar da ta saye ta, inda ake hasashen ko matsala ta samu har ya sa ta kone kurmus.
Wasu daga cikin ma’abota amfani da kafofin sada zumuntar, sun alakanta konewar motar da bakin ciki ko hassadar mutanen kauyen matar, ma’ana dai kamar asiri ne aka yi wa motar har ta kone don bakin ciki.
Shiga wannan link din domin kallon bidiyon: https://web.facebook.com/100006106741919/videos/2813952582151606/