Rundunar tawagar kwanturolan hukumar Kwastam na kasa (NCS), ta kai sumame wasu kasuwanni da manyan dakunan ajiyar kaya a Kudu maso Yammacin Nigeria, inda suka kwace buhunan shinkafa yar kasar waje da sauran kayayyakin da aka shigo da su ba bisa ka’ida ba.
A yayin kai wannan sumame, rahotanni sun bayyana cewa rundunar ta cafke akalla buhunan shinkafa 1,930 masu nauyin 50kg da aka shigo da su ta barauniyar hanya a jihohin Lagos da Ogun.
Kodinetan wannan tawagar, Ahmadu Bello Shuaibu, ya ce wannan sumamen sun yi shi ne domin karfafa guiwar tsarin gwamnatin tarayya na bunkasa noman da amfani da shinkafar gida, da kuma samar da ayyukan yi ta wannan hanyar.
Shu’aibu wanda ya tabbatar da karuwar jiragen da ke tsayawa Nigeria da sunan jiragen kaya marasa laifuka, alhalin suna dauke da haramtattun kaya, ya ce hukumar ta tara akalla N708m daga ire iren wadannan kayan a cikin makonni biyu.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta cafke wasu kayan da suka hada da roll 1,227 na tufafin ‘chiffon’, dila 18 ta turare, kayan shafa da jakunkuna, katon 2,064 na kwan lantarki da kuma katon 1,810 na giya mai bugarwa da maras bugarwa, kuma za su mika su ga gwamnatin tarayya.
Ya bayyana cewa saboda tsauraran matakan da hukumar kwastam ta dauka, masu safarar kaya ba bisa ka’ida ba, sun shiga tsaka mai wuya, musamman wajen safarar shinkafa daga iyakokin kasar.
Masu safarar kayan, a cewarsa, a yanzu suna amdani da mashinan da ake amfani da su wajen yin kabu kabu, amma duk da hakan, hukumar ta dakile su, ta hanasu sakat yanzu.