Bidiyon wasu yara guda biyu suna kwaikwayon yadda kakansu ke tafiya ya ba mutane da dama dariya a TikTok, Legit.ng ta ruwaito.
Yanzu haka, bidiyon ya samu adadin kallo fiye da miliyan 13 a dandalin. 4sunshine Baby ta wallafa bidiyon wanda ya nuna yaran yayin da aka bar su tare da kakansu.
KU KARANTA: Osinbaje ya shilla ƙasar Vietnam don yin ziyararkwanaki 3
A gajeren bidiyon wanda bai wuce sakanni 8 ba, an nuna yadda yaran biyu suke biye da kakansu. An ga yadda tsohon ke tafe su kuma yaran suna biye suna kwafar irin tafiyarsa.
Tabbas sun kwato irin tafiyarsa kuma sun bi shi duk inda zai nufa a harabar gidan. Mutane da dama sun yi ta kallon bidiyon suna kwasar nishadi. Kamar yadda aka wallafa a tsokacin bidiyon:
“Wadannan kananun yaran sun kasance tare da kakansu, yau ma ba su je ko ina ba.”
Zuwa yanzu fiye da mutane dubu 261 ne suka latsa bidiyon, kuma an samu sharhi daga fiye da mutane 3000.
Yadda barin jikin Magidanci ya shanye ɓayan matarsa ta sanar da shi cewa ba shi bane asalin mahaifin yaransu 2
Wani dan Najeriya ya bayyana tashin hankalin da wani mutum ya shiga bayan matarsa ta sanar da shi cewa yaransu biyu ba nashi bane, Legit.ng ta ruwaito.
Kamar yadda @MeverickThamani ya bayyana a shafinsa ba Twitter, mutumin ya kai shekaru 50 da doriya kuma ‘yar uwarsa ce yanzu haka take kulawa da shi a asibiti sanna ita ce ta bayar da labarin abinda ya same shi.