Rundunar Sojin Najeriya ta Operation Lafiya dole ta hallaka yan Boko Haram kimanin 48 tare da ceto wadansu mutane 11 da aka yi garkuwa da su a Jihar Borno.
Wata sanarwa mai dauke da sanya hannun Daraktan dake Kulaq da hulda da jama’a na rundunar Sojin, Birgediya Janar Mohammad Yerima ta ce sojin sun kashe yan ta’adda 11 a wani kwantan bauna da aka yi musu a tsakanin Cibibok zuwa Damboa na jihar ta Borno.
Rundunar ta cimma wannan nasara ce bayan samun bayanan sirri dake nuni da cewa sauran burbushin yan Boko Haram da suka rage a dajin Sambisa suna kokarin neman gurin tsira sakamakon barin wuta da rundunar Operation Lafiya Dolen ke yi.
Yayin wanchan arangama kamar yadda sanarwar ta bayyana an yi nasarar ceto mutane takwas daga hannun yan Boko Haram inda daya daga cikin mutanen ya gamuda mummunar rauni.
Abubuwan da aka kwato hannun yan ta’addan sun hada da Bindiga kirar AK47 da Bindiga mai jigida da dai sauran su.