Wata mata a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba ta tashi wani matashi a Twitter yayin da ya bayyana cewa yana da zone amma bai samu budurwar da zai nemi aurenta ba, LIB ta ruwaito.
Abin ya fara ne bayan wani kwararre a harkar soyayya ya bukaci wadanda su ka yi aure da su gabatar da hotunan aurensu.
KU KARANTA: Yadda budurwata ta rabu da ni bayan na yaba da kyawun wata budurwa a Facebook, Saurayi
Sai dai matashin ya wallafa hoton zobe a hannunsa inda yace na aure ne amma har yanzu be samu matar da zai aura ba.
Ita kuma budurwar bayan ganin haka ne bata yi kasa a gwiwa ba ta tashe shi, inda tace tana da yatsu amma babu zobe a hannunta.
Matashin ya tambayeta idan za ta amince suyi aure inda tace zubinsa ya yi mata sai dai tana son karin bayani akan shi.
Daga nan ne wani ya shawarce su da su nufi bangaren sakonnin kai tsaye don su ci gaba da tattaunawa wanda idan akwai rabon aure sai suyi.
Ya sharbi kuka: Yadda matashi ya kai wa budurwarsa ziyara bazata, ya sha mamakin abin da ya gani
Wani matashi ya sha kuma bayan kai wa budurwarsa ziyarar ba zata inda ya ga abinda yayi matukar daga masa hankali har ya kasa hakuri yayi wallafa a soshiyal midiya, Legit.ng ta ruwaito.
Wannan wallafar ta sa mutane da dama sun dinga kwanta masa da hankali inda su ka ba shi shawarar ya bar ta ya ci gaba da rayuwarsa.
Ya wallafa hirar ne a Twitter inda yace bayan isar sa gidan ba tare da sanar da ita ba, ya dade yana kwankwasa kofa amma be ji amsa ba.