A ranar Laraba ne gwamnatin tarayyan Najeriya, ta bayyana cewa bata da kudurin dakatar da kafafen watsa labarai, duk da cewar tana kokarin samar da wasu dokoki da za su gindaya akan kafafen watsa labaran. Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Ministan watsa labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammad yace kudurin gwamnatin tarayya na samar da dokokin yayi dai-dai da ra’ayin da duniya ke akai yanzu.
Minista Alhaji Lai Muhammad yayi jawabinne a wani taro na kwana biyu wanda hukumar (ARTCO) tare da ma’aikatar habbaka al’adun ta Kasa suka gudanar.
KARANTA:- DA DUMI-DUMI: Kotun Benin ta sanar da cigaba da tsare Sunday Igboho a gidan kurkuku
Kamar yadda Minista Alhaji Lai Muhammad yace, babu wata gwamnatin da zata saka idanu tana ganin makiyanta suna amfani da kafafen watsa labarai suna yakar kasar.
Labaran karya da kafafen watsa labarai suke wallafawa a shafukansu, yayi tasiri sosai wajan kara samar da rashin tsaro da kin bin doka a kasar nan.
Ministan yayi kira ga kafafen watsa labarai da su cigaba da watsa ingantattun, yace a guji yada labarai marasa makama don gudun assasa rikici a cikin kasar nan.
Ministan ya cigaba da cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai cigaba da tallafawa kafafen watsa labarai wadanda suke wallafa ingantattun labarai.
Haka kuma babban Sakataren hukumar ta (NICO). Mista Ado Muhammad Yahuza, yace, kudurin gwamnatin tarayya na wannan shekarar 2021 za ta bada muhimmanci sosai wajan taimakawa kafafen watsa labarai donsu ciyar da Kasar gaba.
Inda yake cewa ” Munyi imani da cewa wasu daga cikin matsalolin matsalolin wannan kasa za’a iya samun daidaiton akansu idan aka baiwa kafafen watsa labarai muhimmanci.”
“Munyi imani da cewa kafafen watsa labarai suna taka muhimmiyar rawa wajan tallata al’adunmu, gami da taimakawa wajan hada kawunanmu, yin wannan zai kara hada kasar nan waje daya, sannan a iya samun damar cinma manufofin da muke dasu a wannan kasar.”