An yi waje rod da sahararriyar yar wasan Tennis din nan na kasar Japan Naomi Osaka bayan da ta sha kashi a jere hannun Marketa Vondrousova.
Tun a minti na 68 ne da aka fatattaki Osaka wacce ita ce ta kunna fitialr gasar a ranar juma’a yayin budewa, lamarin da ya kawo karshen mafarkinta na lashe lambar yabo na zinare a gasar a gida.
“Ya zan bayyana bakin ciki na, gaskiya abin akwai cin rai ba kaɗan ba, babu ko shakka wannan ya fi kuna matuka” cewar gwarzuwar Grand Slam har sau huɗu.
Wannan duka da Osaka ta sha ya zo be yan watanni bayan kauracewarta a gasar French Open da ya biyo bayan rashin halartar taron manema labarai da ta yi, sakamakon abinda ta kira kiyaye lafiyar kwakwalwarta.
Yanzu haka Vondrousova yar asalin ƙasar Czech wacce take matsayi na 42 a duniya zata kece raini ne da yar Argentinar nan Paul Badosa ko kuma yar Sifaniya Nadia Podoroska.