Babban Jojin Najeriya, Mai Shari’a Tanko Muhammad yace Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bai taɓa Katsalandan ba a harkokin Shari’a.
“A dukkanin shekarun da kayi a ofis, babu wani lokaci da Shugaban Ƙasa, ko wani mutum daga gare shi yayi yunƙurin neman wata alfarma a Kotu na ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Rukunin Gidaje 76 A Jihar Jigawa
“Zamu iya tunawa babu wani yunƙuri daga Kai ko kuma a madadin Buhari yayi Katsalandan a wani hukunci na Shari’a,” ya bayyana haka a daren Alhamis.
CJN yayi wannan jawabin a Aso Villa , a lokacin bikin liyafar buɗe baki da Shugaban Ƙasa ya gayyace Shuwagabancin ɓangaren Shari’a na Ƙasa.
Tanko yace ya yarda cewa, babu irin wannan Katsalandan ɗin ga Ministoci da sauran Hukumomin Gwamnati.
Mohammed ya bada tabbacin cewa Masu Shari’u a Kotun Ƙoli, da joji na faɗin Kotu na, suna bakin ƙoƙarin su, wajen yin abinda ya dace a Shari’a.
Babu wata Shari’a da aka tsaida, dukkanin su ana yin su akan lokaci, kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya buƙata, inji shi.
A jawabin shi, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yasha alwashin cewa Sashen Zartaswa zasu cigaba da mutunta Tsarin Shari’a a iyakokin daya kamata su tsaya.
Shugaban Ƙasa ya bayyana mutuntawar shi ga Sashen Zartaswa, yana mai jaddada cewa doka da hukunci a cikin Al’umma za’a iya tabbatar dashi ne kawai, idan ya zamanto anbi Doka.
“Zan cigaba da nesa da kaina daga gareku domin gudun kada ace ina yi maku Katsalandan”, ya shaidawa taron.
Comments 1