Fitaccen Marubucin Littafin nan na Turanci Wole Soyinka ya ƙalubalanci Gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na rashin iya magance matsalolin dake fuskantar Najeriya.
Soyinka yace Najeriya tuni ta fara rarrabewa saboda gwamnati maici a yanzu bata da maganin matsalolin Ƙasar.
Ya bayyana haka a taron Manema labaru a Freedom na Jahar Lagos a ranar Alhamis.

KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Yahaya ya Gabatar da Kasafin Kudin 2022 ga Majalissar Jihar Kogi
Fitaccen Marubucin ya gargaɗi ƴan Najeriya akan jiran samun mafutar matsalolin dake fuskantar ƙasar daga Gwamnati.
A cewar Soyinka ” Matsalar shine gwamnati bata da maganin matsalolin Najeriya. Idan muna kallon wannan Gwamnatin domin samun mafita to mun rasa ta.
“Muna cikin wani hali. Wannan ƙasar na cikin wani hali. Tana wargajewa a gaban idanun mu. Wannnan gwamnati ta faɗi.
Yayi nuni dacewar maganin matsalolin Najeriya shine ƙabilu da dama su zo su haɗa kai, tare da gano hanyoyin da za’a samu haɗin kai.