Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa ma’aikatar kudi da tsare-tsaren kasafin kudi umurnin biyan naira biliyan 600 domin gudanar da wadansu manyan ayyuka cikin wata uku.
Buhari ya ba da wannan umurnin ne cikin jawabinsa da ya yiwa ‘yan kasa domin tunawa da cikar Nijeriya shekara 59 da samun ‘yancin kai a yau Talata. Buhari ya ce ya ba da wannan umurnin ne domin ganin an bunkasa hanyoyin zuba hannun jari a bangaren walwalar al’umma.
A cewarsa kaddamar da kasafin manyan ayyuka na 2019, wanda aka amince a cikin watan Yunijn 2019, za a tabbatar da an gudanar da ayyukan cikin hanzari domin tabbatar da an kammala manyan ayyuka a lokacin da suka dace.
Ya tabbatar da cewa; ya zuwa yanzu gwamnatin tarayya ta saki naira Tiriliyan 1.74 domin kammala wadansu ayyuka cikin shekarar 2018.