Hukumar majalisar dinkin duniya da ke gudanar da ayyukan tallafi a Libya wato UNSMIL, ta yi tir da barazanar da wadansu ‘yan bindiga suka yi ministan kudi na kasar Libya.
Majalisar sun bayyana cewa; hakan babbar barazana ne ga doka. Ta ci gaba da cewa; majalisar na goyon bayan amintattun hukumomi tare da goyon bayansu kan bankado bata gari domin a hukunta su. Kuma sun ce a shirye suke su ba da dukkanin gudummawar da ake bukata ga kasar da jami’an kasar domin ganin an yiwa al’ummar Libya hidima. Tare da ‘yantar da su wajen tabbatar da doka da oda.
A makon da ya gabata ne, wadansu ‘yan bindiga suka dira a muhallin ministan kudi, Faraj Bumtari inda suka yi masa barazana da ya saki kudi ga ‘yan bindiga ta hanyar sanya masa bindiga a kai.
Tuni ministan cikin gida ya ba da umurnin cafko wadannan ‘yan bindigar.