Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayar da umarnin gaggawa domin kubutar da Fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja.
Umarnin shugaban kasar na zuwa bayan da suka dashi kwanaki dari a hannun yan bindigar, da suka yi garkuwa da su, kwanaki 85 da suka gabata.
Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa a ranar 28 ga watan Maris ne yan bindiga Dadi suka yi awon gaba da wasu daga cikin Fasinjojin da suka hau jirgin kasar daga Abuja zuwa Kaduna, bayan sun dasa masa Bom.
A yayin harin mutane akalla 8 sun rasa rayukan su, yayin da dama cikin su suka jikkata, baya ga haka yan bindigar suka yi awon gaba da wasu daga cikin su zuwa inda har yanzu ba a sani ba.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Buhari yace dole ne duk jami’an tsaron kasar suyi aiki Tukuru, domin Ceton mutanan daga wajen yan Garkuwa da su cikin koshin lafiya.
Yanzu haka dai akwai fasinjojin sama da 50 a dake tsare wajen yan Garkuwa, duk da cewa wasu daga cikin su tuni suka kubuta.
Daga cikin wadanda suka kubuta daga baya bayan nan akwai wata mace mai juna biyu data haihu, sai kuma Sadiq Ango Abdullahi da ga shugaban ƙungiyar dattawan Arewa Ango Abdullahi.