Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa kotun koli bisa kwarewar da suka nuna da kuma “sadaukarwa da hakuri” dangane da dawo da Sanata Hope Uzodinma na APC a matsayin wanda ya lashe zaben 9 ga watan Maris din 2019 na gwamnan jihar Imo.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin da yake maida jawabi dangane da hukuncin da kotun koli ta yi na cire Emeka Ihedioha na PDP a matsayin gwamnan Imo ta ayyana Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben.
Shugaban kasa Buhari ya ce; hanyar zuwa adalci tana iya yin tsayi, amma a cewarsa ita kadai ce hanyar da duk wanda yake da wani kalubale zai fuskanta.
“A karkashin sabuwar gwamnatin, sabuwar mikakkiyar hanya wajen gina al’ummar Imo zai fara. Sakamakon wannan nasarar, al’ummar jihar Imo sune wadanda suka yi nasara.” In ji Buhari,
A yayin da yake taya sabon gwamnan Imo murna, Buhari ya shawarci Uzodinma da ya karfafa manufofin APC tare da hada kan ‘yan jihar ta hanyar sanya kowa a cikin gwamnatinsa.