A ranar Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wuce birnin Makkah na kasar Saudiyya domin yin aikin umrah.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, ya ce Buhari da tawagarsa sun yi addu’ar fatan alheri ga Najeriya da al’ummarta, ya kuma maido da zaman lafiya da tsaro a kasar da ma duniya baki daya.
Shehu ya ce an kuma yi addu’o’i ga tattalin arzikin da annobar ta yi barna, domin amfanin kasa da jama’arta.
Ya Kara da cewa, Buhari wanda mataimakin gwamnan yankin, Yarima Sa’ud Al-Faisal ya tarbe shi a filin jirgin saman Yarima Muhammad Abdulaziz da ke Madina, ya dauki lokaci mai yawa a masallacin Annabi Muhammad, masallacin mafi tsarkin a addinin Musulunci na biyu, inda ya rika gudanar da addu’o’i da karatu. na Alkur’ani mai girma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ankama Yan sanda sun kawace kudi a hannun Matafiyi
A ranar Litinin din da ta gabata ne Buhari ya bar Abuja zuwa Riyadh, domin halartar babban taro karo na 5 na zuba jari.
A ranar Laraba ne ya yi dan takaitaccen zango a Madina inda ya gudanar da sallar isha’i tare da gudanar da addu’o’i tare da tawagarsa domin samun zaman lafiya da tsaro a fadin Najeriya da ma duniya baki daya.