Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano.
Fitacciyar jaruma a Masana’antar Kannywwod wacce a ta kware a salon Barkwanci, Zulahat Ibrahim Zpreety, ta bayyana cewar ita fa harkar fim ba za ta Hana ta yin aure ba, don haka a duk lokacin da ta samu mijin da zai aure ta, to za ta yi aure ne.
Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Wakilin jaridar Dimukaradiyya a Kan rayuwar ta a harkar fim, in da ta ke cewa;
“Ita harkar fim a baya ban san zan yi ta ba, Amma tun Ina karama na san wata Rana zan yi aure idan Ina Raye, don haka babu yadda za a yi a ce harkar fim ta Hana ni yin aure.”
Ta Kara da cewar “Shi aure idaba ne Kuma shi ne ya kawo mu duniya don haka an same mu ne ta dalilin aure da iyayen mu suka yi, don haka mu ma ba za mu ki aure ba. Kuma duk yadda Mace ta Kai ga Isa ba za ta zama abin alfahari a wajen iyayen ta ba, har sai a lokacin da ta yi aure.” Inji ta
Daga karshe ta yi Kira ga masoyan ta da su taya ta da addu’ar Allah ya kawo Mata miji nagari, wanda zai zama garkuwa gare ta da ya’yan da za su haifa a duniya da lahira.
Masha Allah muna miki fatan Alkheri