Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon mai ritaya murnar cikarsa shekaru 87, inda ya yi taya shi da iyalinsa murnar tare da yi masa addu’ar samun koshin lafiya da karfin ci gaba da hidimtawa kasa.
Buhari, a cikin sakon taya murna wanda mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata a Abuja, ya jinjinawa Gowon saboda gagarumar gudummawar da ya ke bayarwa wajen ci gaban kasar.
Ya bayyana tsohon Shugaban kasar a matsayin wanda ya kasance a koyaushe yana ba da shawarar zaman lafiya da haɗin kai, kuma yana ci gaba da kasancewa muryar tunani da hikima a cikin kyakkyawan shugabanci da dimokuraɗiyya.
Shugaban ya kuma lurantar tare da yabawa da mika godiya, matsayin Dattijon kasa kuma shugaban “Najeriya tana Addu’a”, wanda hangen nesan sa na na samar da babbar ƙasa ya sanya shi cikin shirye -shiryensa wanda ya ƙaddamar a cikin shekarun 70’s.
Ya bayyana cewa irin wadannan shirye-shiryen sun hada da Hukumar yi wa kasa hidima (NYSC), kirkirar jihohi, da aikin sasantawa, sake ginawa da farfado da aikin, wanda ya zama abin kwatance domin jituwa.
Buhari ya yi imanin cewa alheri da arziki sun ci gaba da jagorantar dattijon, tun daga aikin soja, shugaban ma’aikatan soji mai kananan shekaru kuma shugaban ƙasa, kafin ya zama Farfesa na Kimiyyar Siyasa kuma wanda ya kafa Cibiyar Yakubu Gowon.
Cibiyar ta ci gaba da tallafawa batutuwan shugabanci nagari, shawo kan cututtuka, HIV/AIDS da zazzabin cizon sauro.
Shugaba Buhari ya bi sahun dangin Gowon, abokai da ‘yan Najeriya wajen yi wa shugaban addu’ar tsawon kwana da fatan alheri.