Shugaban Hukumar yaki da rashawa da dangogin su ta kasa ICPC Farfesa Bolaji Owasanoye ya ce shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana da masu dafa masa a siyasan ce, wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da ya yiwa kasar nan katutu.
Owasanoye ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da wata takarda da ya gabatar wajen taron na musamman da ya shafi yaƙi da cin hanci wanda aka shirya shi karkashin wani shiri na musamman tsakanin yan sandan kasa da kasa, da nufin duba kan tsaro, da kuma yadda za a mayar da dukiyar kasar dake jibge a kasashen ketare, wanda taron kuma ya gudana a Abuja.
Shugaban hukumar wanda ya samu wakilcin daraktan ayyuka na hukumar Mr Akeem Lawal, ya kara da cewa gwamnatin Buhari tayi fice wajen aiki kafada da kafada da hukumomin dake yaki da cin hanci a kasar.