Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da aikin ginin Layin dogo da zai taso daga Kano zuwa Kaduna, nan da mako biyu masu zuwa.
Ministan sufuri na Kasa Rotimi Amaechi ne ya bayyana hakan a yau juma’a a babban birnin tarayya Abuja.
Amaechi Wanda ya bayyana hakan a Taron manema Labarai da fadar gwamnatin tarayya ke shirya wa a kowani mako, ya ce, “Dukkannin shirye shirye bada kwangilan sun kammala, kuma bashi da za’a ciyo, domin aikin badaga kasar China ya ke ba, kamar yadda aka tsara a baya,” inji shi.
Ya kara da cewa, ma’aikatar sufuri ta kasa ce, ke da hakkin tabbatar da fitar da kudaden aikin, kamar yadda gwamnatin tarayya ta tsara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ganduje ya halarci Taron da Masarautar Kano ta shirya
Kazalika ya ce, gwamnatin tarayya ta ruga ta biya Dala milliyan dari biyu, da goma sha takwas ($218m) ga yan kwangila, inda ya Kuma ce, za’a sake bai wa yan kwangilan, Dala milliyan dari ($100), wanda jimullar kudin zai kai Dala milliyan dari uku da goma sha takwas ($318m).
” Nan da mako biyu za mu kaddamar da aikin Layin dogo daga Kano zuwa Kaduna, wanda Shugaba Buhari ne zai kaddamar, Kuma za’a fara aikin a nan ta ke” a cewar Amaechi.
A karshe ya ce, Gwamnatin tarayya tuni ta biya naira billiyan sha uku, na aikin Layin dogo da zai tashi daga Fatakwal zuwa Birnin Maiduguri, inda ya Kuma ce, nan bada jimawa ba, za’a kammala biyan sauran ragowar kudaden, da ya kai naira billiyan goma, domin kammala aiki