A wani mataki na nuna godiya da kwarin gwiwa ga gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bisa jajircewarsa a fannin ilimi, tare da ware masa sama da kashi 26 cikin 100 na kasafin kudi na shekarar 2022, hakan ya sanya Jami’ar Bayero Kano (BUK) karkashin tsangayar Ilimi, ta kuduri aniyar karramar gwamnan bisa namijin kwazonsa a shekara mai zuwa.
Farfesa Abdurrashid Garba, wanda tsohon mataimakin shugaban jami’ar BUK ne ya bayyana hakan, a yayin taron shekara-shekara na tsangayar ilimi karo na biyu, wanda kuma shi ne shugaban taron daya gudana a dakin taro na Convocation Arena dake sabuwar jami’ar Bayero a jiya Litinin.
“Mai girma gwamna, muna matukar godiya da nasarorin da ka samu a fannin ilimi, kana yin abin mamaki, wannan jami’a za ta yi bikin murnar cika shekaru 50 a shekara mai zuwa. Sannan kuma za mu taya murna da irin nasarorin da ka samu a Mulkin jihar Kano.”in ji shi.

Babban mai jawabi a wajen taron, Farfesa Mansur Usman Malunfashi, daga Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, bayan ya yaba wa gwamnan bisa yadda yake tallafa wa fannin ilimi, ya yaba da yadda aka ware kashi 26 cikin 100 na kasafin kudi na kasafin kudi na shekarar 2022.

Farfesa Shehu Abdullahi Ma’aji, wanda shi ne Shugaban kwamitin shirya taron, ya yaba wa gwamnan da kasancewar tauraruwarsa na ci gaba da haskaka ta fannin taimakon ilimi.
A nasa jawabin, Gwamna Ganduje ya tunatar da cewa, gwamnatinsa ba ta da wani zabi, illa ta tallafa wa ilimi daga duk wani abin da ya dace.

Yana mai jaddada cewa, “Ilimi abin ci gaba ne, jigon ci gaba ne, don haka dole ne ya himma wajen hidimta masa da yawa.”

Ya kuma kara da gargadin cewa, a koda yaushe hakkin kowa ne, a hada kai wuri guda domin ci gaban ilimi a kasar nan.