By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa tace adadin sabbin masu rajista a ci gaba da rijistar masu kada kuri’a a fadin kasar ya kai Miliyan 3,899,238.
Hakan yana ƙunshe a cikin sabunta rahoton CVR na mako-mako da aka fitar a daren Litinin.
Rugujewar kididdigar da aka yi kafin yin rajista ta nuna cewa jihar Osun ce ta fi kowacce yawan masu rajista ta yanar gizo da 453,949; Sai jihar Delta mai mutane dubu 297,396 sai jihar Bayelsa itama mai mitane dubu 252,534.
Haka kuma, jihar Kebbi na da mutane dubu 23,758,sai Abia dake da dubu 19,308 da Yobe da take da adadin mutane 18,600 bi da bi sune jihohin da mafi ƙarancin rajista ta yanar gizo a CVR.
Rahoton ya kara da cewa, “Yawancin wadanda suka kammala rajistar ta yanar gizo da kuma na zahiri sun kai miliyan 1,509,989, wadanda suka kunshi maza guda dubu 769,359 da mata dubu 740,630 daga cikinsu akwai dubu 15,903 wadanda sun kasance nakasassu ne.
Sabuntawar ta kuma nuna cewa dubu 575,380 na masu rajista sun yi rajista ta kan layi, yayin da dubu 934,609 suka kammala aikin ta hanyar rajistar jiki.An kuma lura da cewa miliyan 3,204,729 na aikace-aikacen sun fito ne daga maza miliyan 2,735,838 daga mata dubu 66,238 da kuma nakasassu.
A cewar rahoton, ya zuwa lokacin da aka fitar da sanarwar, mutane miliyan 5,940,567 ne suka nemi a canza musu katin zabe na dindindin, sun bukaci a maye gurbin PVC, da sabunta bayanan masu kada kuri’a da dai sauransu.