Tsohon shugaban rundunar sojin kasar nan Laftanar Janar Yusif Tukur Buratai ya nesanta kansa da duk wata kadara da ake danganta shi da ita a yankin Wuse dake Abuja.
A baya ne dai aka samu labarin cewa jami’an hukumar ICPC sun yiwa gidan sa dake yankin na Wuse kawanya, domin dai tafiya da shi.
Buratai a wata Sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimaka masa Osuagwu Ugochukwu ESQ, ya bayyana labarin da cewa wani ƙage ne, da ake son yin amfani da shi wajen batawa mai gidan nasa suna.
A baya bayan nan dai wata jarida da ake wallafa ta a Intanet ta wallafa cewa jami’an Hukumar ICPC sun yiwa gidan Buratai dake Abuja kawanya.
Jaridar ta kara da cewa an samu kudi kimanin Naira biliyan 1.85, lokacin da suka farwa gidan tsohon shugaban rundunar sojin.
A karshe ya bukaci al’umma da suyi watsi da rahoton cewa an samu abinda ake zargin na Buratai ne, sannan kuma bashi da gida a wajen da ake ikirarin cewa hakan ya faru.