Hukuma ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afrika wato CAF ta fitar da ranar da za’a ci gaba da fafata gasar ajin zakaru ta nahiyar Afrika wato ƙarashen kakar wasa ta 2019 zuwa 2020 tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa guda 4.
Tun a watannin baya dai aka dakatar da gasar biyo bayan ɓullar cutar nan ta Coronavirus da ta addabi duniya inda daga ciki hadda nahiyar ta Afrika daga cikin nahiyoyin da ake dasu a duniya.
Ga yadda hukumar ta CAF ta fitar da jaddawalin buga ragowar wasannin:
1. Za’a fafata wasan farko na wasan kusa dana ƙarshe a ranakun 16 da 16 ga watan Oktoba na shekarar 2020 inda za a buga wasannin a ƙasar Morocco.
2. Za a fafata wasan zagaye na biyu a ranakun 23 da 34 ga watan na Oktoba a ƙasar Masar.
Sannan kuma dukkanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da suka sami nasarar zuwa wasan ƙarshe zasu fafata wasan na ƙarshe a ranar 6 ga watan Nuwamba.
Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa guda 4 ne dai suka rage a gasar wato guda biyu daga ƙasar Masar guda biyu kuma daga ƙasar Morocco.