Canada Ta Hana Shiga Kasar Daga Nigeria Saboda Dakile Cutar Corona Samfarin Omicron
Kasar Canada ta sanya dokar hana shiga kasar daga Najeriya a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar Corona Samfarin Omicron.
Kasar da ke Arewacin Amurka da ke da kwararar bakin haure daga Najeriya ta sanar da hakan a safiyar yau Laraba.
Gabaɗaya, hukumomin Canada sun haramtawa ƙasashe 10 shiga kasar Saboda yunkurunsu na dakile COVID-19.
Kasashen Afirka ta Kudu da Namibiya da Lesotho da Botswana da Eswatini da Zimbabwe da Mozambique da Najeriya da Malawi da Masar na daya daga cikin kasashen da Dokar zata shafa.
Ministan Sufuri na Canada Omar Alghabra, ya ce ‘yan kasashen waje da suke kokarin shiga kasar a cikin kwanaki 14 masu zuwa, an hana su shiga Canada na wani dan lokaci.
Ya kara da cewa ‘yan kasar Canada da mazaunan dindindin wadanda suka kasance a cikin kasashe 10, har ma da wadanda suka yi cikakken rigakafin, dole ne a gwada su kafin su shiga Canada.
An kuma bayar da rahoton cewa Birtaniya, Columbia ta gano kwayar cutar na sabon nau’in, wanda mutanann suka dawo daga Najeriya kwanan nan.
A ranar Laraba, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta sanar da cewa an gano wasu nau’ikan nau’ikan Omicron guda biyu a cikin kasar.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana wayar cutar Omicron na COVID a matsayin “haɗari mai girma”.
A halin yanzu ba a san yadda kwayar cutar ke yaduwa ba.
Comments 2