- Wasu ‘yan takarar jam’iyyar PDP na mazabar Lokoja I da II Hon Ahmed Shehu Yabagi da Hon. Ishaiku Kashim Musa sun fice daga jam’iyyar sun koma APC.
- APC ta bayyana jin dadinta game da matakin da ‘yan siyasar suka dauka na shiga jam’iyya mai mulki.
- An bukaci masu sauya shekar dasu kara karfafa gwiwar magoya bayansu da su yi aiki tukuru domin samun nasarar jam’iyyar.
Gabanin zaben gwamna da za a yi a watan Nuwamba, ‘yan takarar jam’iyyar PDP na mazabar Lokoja I da II Hon Ahmed Shehu Yabagi da Hon. Ishaiku Kashim Musa sun fice daga jam’iyyar sun koma APC,Daily Post ta rawaito.
Gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello ne ya tarbe su.
KARANTA WANNAN: CireTallafin fetur: Taron FG da NLC Ya Ƙare Ba Tare Da Cimma Matsaya Ba
Gwamna Bello ya bayyana jin dadinsa game da matakin da ‘yan siyasar suka dauka na shiga jam’iyya mai mulki.
Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa tana girmama iya aiki, kuma ba lallai ba ne wanda ya dade a jam’iyya mai mulki.
Ya kuma shawarci ’yan siyasa da su zo da dukiyoyinsu na kwarewa, ya kuma kara da cewa ya kamata su kara karfafa gwiwar magoya bayansu da su yi aiki tukuru domin samun nasarar jam’iyyar.
A jawabansu na daban, sabbin masu shiga jam’iyyar APC sun baiwa gwamnan tabbacin yin aiki bisa tsarin sabon gidan siyasar su.
A halin da ake ciki, Dan takarar Sanata na Accord na Kogi ta Yamma a zaben 2023, Bashorun Moses Eseyin ya fice daga jam’iyyar.
Eseyin dai bai bayyana dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar Accord Party ba.
Ficewar tasa na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazaba 6 a karamar hukumar Mopamuro ta jihar Kogi.
Wasikar ta kasance mai kwanan wata 31 ga watan Mayu, 2023.
A wani labarin kuma, NSA da NAFDAC Zasu Hada Gwiwa Don Magance Shaye-Shayen Muggan Kwayoyi
Ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya kulla hadin gwiwa da hukumar NAFDAC domin dakile amfani da miyagun kwayoyi a fadin kasar nan.
NSA ta ce amfani da miyagun kwayoyi na haifar da rashin tsaro a kasar nan.
NAFDAC ta yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su tona asirin masu sayar da miyagun kwayoyi a kasar nan.