- Hukumar tsaro ta farin kaya Civil Defence ta Najeriya ta tura jami’anta zuwa gidajen man fetur domin tabbatar da cewa an siyar da man da ake da shi na PMS ga jama’a.
- Daukar matakin ya biyo bayan tashin gwaron zabbi da man fetur yayi cikin kankanin lokaci.
- Hukumar ta kuma umarci jami’anta da su kamo duk wanda ke sayar da man fetur a kasuwar bayan fage.
Hukumar tsaro ta farin kaya Civil Defence ta Najeriya ta tura jami’anta zuwa gidajen man fetur a Kuros Riba domin tabbatar da cewa an siyar da man da ake da shi na PMS ga jama’a.
Samuel Fadeyi, Kwamandan NSCDC na jihar ne ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Alhamis a Calabar.
KARANTA WANNAN: Zaben gwamna: Wasu ‘Yan Takarar Majalisa na PDP Sun Koma APC
A baya NAN ya bayar da rahoton rufe wasu gidajen man da ke jihar tare da dawo da hada hadar kasuwar mai ta bayan fage a titunan jihar, bayan jawabin da shugaban kasa ya yi a ranar Litinin da ta gabata cewa an cire tallafin.
Wannan aika-aika da dillalan man fetur a jihar suka yi ya jawo wa jama’a wahalhalun da ba za a iya mantawa da ita ba, domin da yawa sun makale a tashoshin mota saboda rashin samun motocin da za su kai su inda suke so.
Fadeyi wanda ya bayyana cewa babu inda za a yi a a bar PMS a kasuwannin bakar fata ya cigaba da ciwa jama’a tuwo a kwarya, ya kuma yi kira ga jama’a da kada su shiga saye da firgici.
“Na aika da jam’aina zuwa gidajen sayar da man fetur domin tabbatar da cewa an sayar da hajoji ga jama’a; wannan ƙirƙira ta karancin mai ta wucin gadi ba a yarda da ita ba.
“Tun daga shekarar 2022, an ba da sanarwar cewa za a fara cire tallafin daga watan Yunin 2023, gwamnatin tarayya ta ce a karshen watan Yuni, za a yi cikakken kayyade kayan.
“Haka zalika, ina da tabbacin gwamnati na kokarin samar da hanyoyin kwantar da tarzoma domin ganin an shawo kan al’amarin cewa cire tallafin zai jawo wa mutane da dama wahalhalu, don haka, ina kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri yayin da ake kokarin shawo kan matsalolin,” inji shi.
Fadeyi ya kuma ce, ya umarci mutanensa da su kamo duk wanda ke sayar da man fetur a kasuwar bayan fage.
Kwamandan ya bukaci jama’a da su kai rahoton ayyukan masu sayar da man fetur a kasuwannin bakar fata ga rundunar (NAN)
A wani labarin kuma, CireTallafin fetur: Taron FG da NLC Ya Ƙare Ba Tare Da Cimma Matsaya Ba
Taron da aka yi tsakanin FG da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC kan batun cire tallafin man fetur bai cimma matsaya ba.
NNPCL, ya tabbatar da karin farashin man fetur na PMS a gidajen sayar da man fetur a fadin kasar nan.
Lamarin ya biyo bayan jawabin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi na cire tallafin man fetur.